Ministocin Larabawa sun bukaci Assad ya bar Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bashar Al assad yana rantsarda ministan tsaro

Ministocin hulda da kasashen waje na kasashen Larabawa sun yi kira ga shugaban Syria Bashar al-Assad, da ya gaggauta sauka daga mulkinsa, tare da yi masa tayin fitarda shi daga kasar lafiya tare da iyalinsa.

Ministocin wadanda suka kammala wani taron gaggawa a Qatar sun kuma bukaci 'yan adawar Syria su kafa gwamnatin rikon kwarya.

Sai dai shugaban kasar Syrian ya umarci dakarunsa da su kara zage damtse kan mayakan 'yan tawayen da ke Damascus, babban birnin kasar da kuma Aleppo, birni na biyu mafi girma a kasar.

Dakarun gwamnatin sun kwato unguwanni biyu a Damascus daga hannun 'yan tawayen kuma gidan talabijin na hukuma yace wasu daga cikin wadanda aka kashe sojin haya ne daga kasashen larabawa.

Karin bayani