Wasu 'yan sanda sun koma Taleban a Afghanistan

Wani mayaki dan Taleban
Image caption Wani mayaki dan Taleban

Hukumomi a Afghanistan sun ce wani kwamanda a rundunar 'yan sandan kasar ya sauya sheka zuwa bangaren 'yan Taliban, tare da wasu mabiyansa su goma sha uku, a yammacin Afghanistan.

Wadanda suka koma bangaren Taliban din sun yi hakan ne da makamai da kuma manyan motoci kirar Amurka.

A kwanakin baya an fatattaki mayakan Taleban daga wannan yanki na Farah.

Wani mai magana da yawun gwamnan lardin Farah ya ce ranar Lahadin da suka wuce ne 'yan sandan suka bar wurin da aka girke su, a wani wurin binciken ababen hawa.

Akwai rahotanin dake cewa kwamandan ya baiwa wasu 'yan sanda bakwai da suka ki binsa guba.

Gwamnatin Afghanistan dai na ta kokarin karfafa rundunar 'yan sandan kasar, rundunar da ake yi ma kallon mai muhimmancin gaske a tsarin tabbatar da tsaro ,bayan dakarun kasashen waje sun janye daga kasar ta Afghanistan a shekara ta dubu biyu da sha hudu.

Karin bayani