Iyalan dan adawar Cuba sun ce kashe shi aka yi

Hakkin mallakar hoto Raquel Perez
Image caption Jagoran 'yan adawar Cuba Oswaldo Paya wanda ya mutu ranar Lahadi

Iyalan dan adawar Cuban nan wanda ya mutu a cikin wani hadarin mota ranar Lahadi Oswaldo Paya, sunce sun yi imanin cewar an ture motarsa ne ta saki hanya.

A wajen taron jana'izar sa wadda daruruwan mutane suka halar ta dan sa ya shaidawa BBC cewar mahaifinsa ya kwashe shekaru yana karbar sakonnin barazanar kashe shi.

Wata sanarwar gwamnatin Cuba dai ta ce motar sa ce ta kwacewa direba ne ta saki hanya inda ta bugi wata bishiya.

Sai dai Dan mamacin wanda shima sunansa Oswaldo ya shaidawa BBC a birnin Havana cewar wasu 'yan kasashen waje biyun da suka tsira da ransu sun ce da gangan aka ture motar da suka tafiya ciki ta saki hanya.

Binciken 'yan sanda

Yanzu dai 'yan sanda sun kaddamar da bincike kan lamarin, amma ofisoshin jekadancin kasashen da mutanen biyu suka fito watau Spain da Sweden basu tabbatarda da'awar da iyalin nasa keyi ba.

Mr. Paya dai ya daina fitowa a fili sosai a 'yan shekerun nan. Amma duk da hakan an tuna shi cikin shauki a wajen jana'izar tasa.

Daruruwan mutanen da suka hallara a Cocin San Salvador Parish Church dake birnin Havana sun tashi tsaye sa'adda ake shigowa da akwatin da gawarsa ke cikin tare da zubarda hawaye daga baya kuma sai wuri ya barke da tafi na tsawon mintuna takwas

Kuma da aka kammala adduoin suka sake barkewa da tafi tare da rera taken kasar Cuba kuma suka yi ta kiran 'yanci-'yanci.

Karin bayani