Shugaba Atta Mills ya riga mu gidan gaskiya

John Atta Mills Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Marigayi Shugaba John Atta Mills

Shugaba John Atta Mills na Ghana ya riga mu gidan gaskiya jim kadan bayan ya kamu da rashin lafiya ranar Talata.

Wata sanarwa daga Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa, "Muna bakin cikin sanar da mutuwar shugaban Jamhuriyar Ghana ba zato ba tsammani".

Rahotanni sun ce Babban Jami'i a Fadar Shugaban Kasar, Henry Martey Newman, ya yi wa al'ummar kasar jawabi ta gidajen talabijin na GTV da TV3 yana cewa Mista Mills ya rasu ne a Asibitin Soji na 37 da ke birnin Accra.

A watan Yuni ya kai ziyara Amurka don a duba lafiyarsa—wadansu rahotanni sun ce ya jima yana fama da sankarar makogwaro.

Ranar Asabar din da gabata ne dai Atta Mills ya yi bikin cika shekaru sittin da takwas da haihuwa.

Ya taba zaman mataimakin shugaban kasa a karkashin Jerry Rawlings.

Sau uku Atta Mills ya tsaya takarar shugabancin kasar Ghana kafin ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben da aka gudanar a 2008, yana kuma da aniyar sake neman darewa kujerar shugabancin a karo na biyu a watan Disamba.

Bayan hawansa mulki, Atta Mills ya fara aiwatar da wani shirin tsuke bakin aljihu, sannan kuma a lokacinsa kasar ta fara samar da man fetur.

Shugaba Mills dai ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta yi amfani da kudaden da za a samu daga man ta hanyar da ta dace.

Ya kwashe akasarin rayuwarsa ta aiki yana karantarwa a Jami'ar Ghana. A Kwalejin Nazarin Gabashin Duniya da Nahiyar Afirka ya yi digirinsa na uku, kafin ya je Jami'ar Stanford dake Palo Alto, California a Amurka don kara zurfafa iliminsa ta hanyar gurbin karo ilimi na Fulbright.

Ya kasance yana kula da lafiyarsa sosai, kuma ya kan yi linkaya, da kwallon kafa, da kuma kwallon gora.

Kundin Tsarin Mulkin kasar dai ya nuna cewa Mataimakin Shugaban Kasa John Dramani Mahama ne zai zama shugaba na rikon kwarya, a kasar da ake yiwa kallon abar koyi ta fuskar dimokuradiyya a Yammacin Afirka.