Shugaban kasar Ghana ya riga mu gidan gaskiya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni daga Ghana sun ce Shugaba John Atta Mills ya riga mu gidan gaskiya.

Wakilin BBC a Accra ya bayyana cewa yanzun nan gidan rediyon kasar ya bayar da labarin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ya samu wata sanarwa daga Ofishin Shugaban Kasa mai tabbatar da mutuwar tasa.

Sanarwar ta ce: "Muna bakin cikin sanar da mutuwar shugaban Jamhuriyar Ghana ba zato ba tsammani".

A cewar sanarwar, shugaban kasar mai shekaru sittin da takwas a duniya ya mutu ne sa'o'i kadan bayan ya kamu da rashin lafiya.

A shekarar 2009 ya zama shugaban kasa; ya kuma taba zama mataimakin shugaban kasa a karkashin Jerry Rawlings daga 1997 zuwa 2001.

Za mu kawo muku karin bayani da zarar sun samu.