'Yan sandan Cuba sun kama kusoshin 'yan adawa 7

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daya daga cikin kusoshi 'yan adawar da aka kama Guillermo Farinas

'Yan sandan Cuba sun kama akalla masu fafutuka 7 saboda rera taken adawa da gwamnatin kasar a lokacin jana'izar fitaccen dan adawan nan Oswaldo Paya, wanda ya mutu a hadarin mota ranar Lahadi.

Daga cikin wadanda aka kaman har da fitaccen mai rajin kare hakkin bil adama, Guillermo Farinas.

Gwamnatin Cuba dai na ganin Amurka ce ke biyan dukkan masu sukarta domin kassara tsarin gurguzun da ake bi a tsibirin.

sai dai kafin mutuwarsa Oswaldo Paya ya sha jaddada cewar shi bai taba karbar kudin Amurka ba kodayake ya kwashe shekaru yana gwagwarmayar mayar da Cuba bisa turbar dimokradiyya.

Karin bayani