An rantsar da sabon shugaban kasar Ghana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Marigayi shugaba John Attah-Mills na Ghana

An rantsar da mataimakin shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama a matsayin sabon shugaban kasa, bayan mutuwar shugaba John Atta-Mills.

Mr. Atta-Mills ya rasu ya na da shekaru sittin da takwas a ranar talata.

Mr. Mahama dai zai kammala wa'adin mulkin Atta-Mills ne kafin zaben da za a gudanar a watan Disamba mai zuwa.

A jawabinsa na farko, sabon shugaba John Mahama ya jinjinawa Mr. Atta-Mills wanda ya sha fama da sankarar makogwaro kafin mutuwarsa a wata asibitin soji.

''Wannan ce ranar da tafi kowacce bakin ciki a tarihin kasarmu. Ban taba tsammanin cewa wata rana zan yi wa al'ummar kasa jawabi a cikin irin wannan mawuyacin hali ba.'' Inji sabon shugaban.

Zaman makoki

Babbar Alkalin kasar Mrs. Geogina Wood ce ta rantsarda sabon shugaban a gaban majalisar dokokin kasar bayan da 'yan majalisar suka yi tsit na tsawon minti daya.

Wakilin BBC a Accra babban birnin kasar Iddi Ali yace kuma tsit din ake ji a kusan ko ina a kasar saboda kaduwar da al'ummarta suka yi bayan samun sanarwar mutuwar shugaban.

''Wasu dama sun saka babaken riguna da jajayen kyallaye kuma babu abinda kake ji a wasu wuraren sai bushe-bushe irin na zaman makoki.'' inji shi.

Sakonnin ta'aziyya

A halin da ake ciki dai shugabannin kasashen duniya sun fara aikewa da sakonni ta'aziyyar su ga kasar kan mutuwar shugaban, John Attah-mills.

Shugaba Barack Obama na Amurka a cikin wata sanarwa yace samun labarin mutuwar Shugaba John Evan Attah-Mills na Ghana ya zo masa da matukar nadama.

Mr. Obama yace ''kodayaushe zan cigaba da tuna ziyararda na kai a Ghana a shekara ta 2009 da irin karimcin da Shugaba Mills da al'ummar Ghana suka nuna min da mata ta Michelle da 'ya'ya na Malia da Sasha da kuma 'yan rakkiya ta.''

Sai dai yace shima yana farin cikin da ya karbi bakuncin Shugaba Mills a can Amurka a farkon wannan shekara.

Shugaban na Amurka wanda ya baiyana Marigayi Attah-Mills da ''rikakken mai goyon bayan mutunta hakkin bil'adama,'' yace ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Ghana sa'adda duniya ta shiga matsin tattalin arziki kuma ya karfafa tushe tsarin dimokradiyyar kasar ta Ghana.

Shugaba Obama yace amadadin al'ummar Amurka yana aikewa da ta'aziyya ga jama'ar Ghana kan mutuwar shugaba nasu kuma ya na kara jaddada cewar zai rike zumuncin dake tsakanin kasashen biyu masu bin tafarkin dimokradiyya wanda shugaba Mill ya taimaka wajen karfafawa.

Shugaban Najeriya Good Luck Jonathan a cikin sanarwar da kakakinsa Dr. Reuben Abati ya fitar yace ya kadu da samu labarin mutuwar Shugaba John Attah-mills.

Sanarwar tace Mr. Jonathan amadadin kansa da jama'ar Najeriya yana mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan shugaba Atta-mill da kuma gwamnati da al'ummar Ghana.

Shugaba Jonathan yace yana fatan kyakkyawar dangantakarda ta wanzu tsakanin kasar sa da Ghana lokacin mulkin Shugaba Mills za ta kara karfafa karkashin jagorancin sabon shugaban kasar ta Ghana domin anfanin kasashen biyu.

Shugabar Liberiya Ellen Jonhson Sirleaf a nata jawabin kan mutuwar Mr. John Attah-mills tace labarin mutuwar tasa yazo mata da ba-zata.

Mrs. Sirleaf a lokacinda take aikewa da sakon ta'aziyyar ta zuwa ga makwabciyar kasar ta watau Ghana tace Mr. Mills ya bayarda muhimmiyar gudumuwa wajen tarrukan kasashen yankinsu na yammacin Afrika da suke halarta akai-akai.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya jijinawa Marigayi John Attah-mill kan iya mulkinsa inda yace ya kasance cike da alhini bayan samun labarin mutuwarsa.

A yayinda yake aikewa da ta'aziyyar sa ga Jama'ar Ghana Mr. Ban yace za a cigaba da tunawa da Mr. Mills kan kyakkywan shugabanci da kuma aiki tukuru da yayi wa kasarsa, inji wata sanarwa da mai magana da yawunsa Martin Nasirky ya fitar.

Mr. John Attah-mills wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar zamanin mulkin tsohon shugaban sojin kasar Jerry Rawlings ya kasance shugaban kasar na farko da mutu akan mulki tun bayan samun 'yancin kan kasar a shekarar 1957.

Karin bayani