Mun kadu da jin mutuwar Atta Mills —JJ Rawlings

Marigayi John Atta Mills Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Marigayi Shugaban kasar Ghana John Atta Mills

Tsohon shugaban kasar Ghana, John Jerry Rawlings, ya bi sahun shugabannin duniya wajen bayyana alhininsa da mutuwar Shugaba John Atta Mills.

A wata tattaunawa da ya yi da wakilin BBC a Brazaville, Mista Rawlings ya ce ya kadu matuka.

“Ni da mai-daki na mun kadu matuka, amma kuma mutuwarsa ba ta zo mana da ba-zata ba, saboda ya jima yana fama da cutar ta sankara”, inji Mista Rawlings, wanda ya kara da cewa, “Sai dai kuma ina ganin a wannan lokaci mutuwarsa ta yi gaggawar zuwa idan aka yi al'akari da cewa a watan Disamba za a gudanar da zabe”.

Da aka tambaye shi ko me yake ganin Mista Atta Mills ya bari wanda za a rika tunawa da shi a Ghana, sai ya ce:

“Ya yi iya bakin kokarinsa; A matsayinsa na mataimaki na ina ganin yana cikin wadanda suka yi fice wajen aiki tukuru. Amma kuma kasancewar cutar ta shafi kunnuwansa da idanuwansa, ya kasance ba ya iya aikin fiye da sa'o'i uku a yini.

“Hakan kuma dole ne zai shafi gudanar da ayyukansa—shi ya na ke ganin da ya yi abin da ya fi wanda ya yi.

“Abin takaicin dai shi ne ba a sake bincika wadansu daga cikin kashe-kashen da aka yi kafin mu hau mulki ba; na so a ce ya gudanar da bincike. Amma dai bari mu jira mu ga abin da za a iya yi a dan lokacin da ya saura”.

Sai dai kuma dangane da sabon shugaban kasar John Mahama, Mista Rawlings cewa ya yi ba shi da masaniya a kan ko yana da hangen nesa da kwarjinin da zai iya ciyar da Ghana gaba.

Karin bayani