Dubban sojojin Syria 'sun nufi birnin Aleppo'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojan Syria suna faretin karrama abokan aikin su da suka mutu

Rahotanni daga Syria sun ce dubban dakarun gwamnati sun tunkari birnin Aleppo wanda shi ne na biyu a kasar, da nufin kwato wuraren da 'yan tawaye su ka karbe.

Rundunar mayakan 'yan tawaye ta Free Syrian Army tace dubunnan sojoji ne da tankunan yaki ke kwarara zuwa Aleppo bayanda su ka baro lardin Idlib da ke daura da iyakar Syria da Turkiyya.

A ranar Talata wakilin BBC da ke wajen birnin Ian Pannell ya ga wasu jiragen yaki da suka yi kama da samfurin kirar Rasha su na luguden wuta kan 'yan tawayen da ke gabashin birnin.

Yace an kwashe matattu da wadanda suka jikkata zuwa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na wucin gadi; inda ya kara da cewar yayinda asarar rayuka ke kara tsananta a wanann yaki, a baiyane take cewa babu wani bangare da ke shirin sallamawa dayan.

Karin bayani