An ji harbe-harbe a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto s
Image caption Maiduguri na yi fama da hare-hare

A Najeriya, rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno na cewa an ji karar harbe-harbe a wasu sassa na birnin kafin sallar Juma'a.

Wasu mazauna birnin sun shaida wa BBC cewa sun ji karar harbe-harbe a kusa da masallacin mai saje, da Zajeri, da kuma Gwange da ke tsakiyar garin.

Rundunar Tabbatar da Tsaro-JTF, ta bakin kakakinta, Laftanal Kanal, Sagir Musa, ta ce har yanzu ba ta da labarin abin da ke faruwa, amma nan gaba kadan za ta yi bayani idan ta samu cikakken bayanin lamarin.

Birnin na Maiduguri ya dade yana fuskantar hare-hare da akasari 'yan kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ke daukar alhakin kaddamarwa.