Akwai dakarun Birtaniya a Somalia

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Taswirar Somalia

Ma'aikatar tsaron Burtaniya, a karon farko ta tabbatar cewa akwai wasu jami'an tsaronta a cikin kasar Somalia.

Ma'aikatar ta ce yanzu haka wasu jami'an sojinta goma suna aikin bada shawara a Hedkwatar rundinar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Afruka dake Mogadishu, babban birnin kasar ta Somalia.

Wakilin BBC ya ce wadannan jami'an na Burtaniya ba su da hurumin shiga yaki, amma wasu daga cikinsu sun kasance a garin Afgoye na Yammacin Mogadishu, mai mhuimmancin gaske, wanda sojojin gwamnati suka kwato daga hannun mayakan kungiyar al Shaba'ab a kwanakin baya.