China: An tuhumi Gu Kailai da aikata kisa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gu Kailai da maigidanta

Kamfanin dillancin labaran China, Xinhua, ya ce an tuhumi matar wani tsohon jigo a jamiyyar Kwaminisanci mai mulki a kasar, Gu Kailai, da laifin aikata kisa da niyya.

Kamfanin na Xinhua ya ce a kwanan nan ne aka gabatar da tuhumar a wata kotun kasar ta China a kan Gu Kailai din da kuma wani mai yi masu hidima, kuma za'a fara sauraren shariar a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Ana dai gudanar da bincike a kan mutanen biyu ne dangane da kisan wani dan kasuwar Birtaniya a China, Neil Heywood.

Al'amarin dai ya kai ga korar maigidan Gu Kailai, watau Bo Xilai daga mukaminsa na shugaban jam'iyyar Kwaminisanci a garin Chong-qing.