An dage takunkumin yin tafiya kan iyalin Taylor

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor a gaba kotun duniya

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsame sunayen wasu tsofaffin jami'an gwamnatin kasar Liberia tare da iyalan tsohon shugaban kasar Charles Taylor 17 daga cikin jerin wadanda aka haramta musu yin tafiye tafiye zuwa sauran kasashen duniya.

Tun a farkon shekarar 2002 ne dai aka sanyawa jami'an haramcin tafiye tafiyen, a wani bangare na takunkumin da aka sanyawa gwamnatin Charles Taylor a wancan lokacin.

Duk da cewa Mr Taylor ya sauka daga kan mukaminsa fiye da shekaru goma da suka gabata, ba'a dage haramcin tafiye tafiyen ba har sai bayan da wata kotu ta musamman dake Birnin Hague ta yanke masa hukunci, bayan ta same shi da aikata laifuffukan yaki.

A makon jiya Mr. Taylor ya daukaka kara kan hukumcin da kotun ta yanke masa da hada da daurin shekaru 50.