Yawaitar bindiga a hannu Amurkawa ya dami Obama

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Amurka Barrack Obama lokacinda ya ziyarci garin Aurora inda aka yi harbe-harben

Shugaba Barack Obama ya sha alwashin yin aiki tare da manyan jam'iyyun Amurka a majalisar dokokin kasar da kuma shugabannin al'umma domin cimma matsaya kan rage yawan kai hare-hare da bindiga kan jama'a a kasar.

Mr. Obama yayi wannan kalamin ne wajen wata yekuwar neman zabe a jahar New Orleans kwanakki bayan da wani dan bindiga-dadi ya bindige mutane akalla 14 a wani gidan sinima da ke jihar Colorado.

Shugaban na Amurka yace zai yi duk abinda hankali zai dauka wajen fitarda bindigogi daga hannun miyagun mutane da kuma marasa hankali a kasar.

''Mun san mallakar bindiga al'adar Amurkawa ce ta kaka da kakanni amma na tabbatar; da yawa daga cikin wadanda suka mallaki bindiga za su amince da ni cewa bindigar AK47 tafi dacewa da hannun soji ba wai masu aikata laifuka ba.''inji shi.

Karin bayani