Ana gwabza fada a birnin Aleppo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojan Gwamnati a wata Unguwa dake birnin Aleppo

Rahotanni daga Syria sun ce ana can ana cigaba da gwabza fada a birnin Aleppo da ke arewacin kasar yayin da karin sojan gwamnati suka tunkari birnin domin taimaka wa wajen kawar da 'yan tawayen da suka kama wadansu unguwanni a can.

Kafafen watsa labaran Gwamnati sun bayar da rahoton cewa sojojin gwamnati sun yi arangama dana 'yan tawaye a unguwar Sakhour inda suka kashe adadi mai yawa na 'yan tawayen tare da kama wasu mutane a zaman fursunonin yaki.

Majiyoyin 'yan adawa sun ce sojan gwamnati na harbi daga boye tare da harba bama-bamai a daidai lokacin da sojojin rundunar 'yan tawaye ta Free Syrian Army ke kokarin fadada unguwannin da suka kama.

Wakilin BBC, Jim Muir, ya ce ga alama har yanzu fadan na birnin Aleppo bai kankama ba saboda rahotannin da ke cewa karin tankunan yaki da kuma sojojin gwamnati na tunkarar garin daga birnin Hama da ke arewa ga birnin na Aleppo.

Haka kuma rahotanni sun ce an gwabza fada a wajen Damascus, babban birni kasar daga kudu .

Masu fafutuka sun ce fiye da mutane 130 aka kashe a fadan ranar Laraba adadin bai hada da wadanda aka kashe daga bangaren gwamnati ba.