Hannayen-jarin Facebook ya fadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Facebook

Hannayen jari a shafin nan na sada zumunta Facebook sun karye bayan ya buga sakamakon farko tun lokacinda ya sayar da hannayen jarin sa a cikin watan Mayu.

Wakilin BBC kan al'amurran kasuwanci ya ce masu hannayen jaari sun daamu cewar bai rigaya ya yi nazarin yadda za a samu kudi ba daga mutanen dake amfani da shafin na Facebook a wayoyin su na salula.

Zuckerberg wanda ya kirkiro shafin na facebook ya gaya wa masu hannayen jari cewar ana bukatar tallace-tallace an shafin muddin ana son ya yi farin jini.

Kamfanin dai ya fara sayar da hannayen jarin ne a baya bayannan inda akai ta ribibin sayan sa.

Karin bayani