Ana daf da bude gasar Olympics

Wasannin Olampiks
Image caption Wasannin Olampiks

Yanzu haka dai an kammala dukkan shirye-shirye domin soma gasar wasannin Olympics a birnin London.

Kuma Pira ministan Burtaniya, David Cameron ya ce kasarsa ta shirya domin daukan bakuncin gasa mafi girma a duniya, gabannin bikin bude gasar wasannin Olympics da zaa yi nan gaba a yau.

Mr Cameron ya ce gasar, wani abun alfahari ne ga Burtaniya, kuma ya kamata jama'ar kasar su karbe ta hannu biyu-biyu.

Tun farko dai an kada karaurrawa a sassa daban-daban na kasar, kuma an yi ta yawo da wutar gasar wasannin na Olympics a kan kogin Thames a cikin wani jirgin ruwa na Gidan Sarauta da aka kawata da gwal.

Karin bayani