An fatattaki 'yan tawayen M23 a Congo

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Yan tawaye a Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarun ta a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sun taimaka wajen fatattakar 'yan tawaye na kungiyar M23 daga garuruwa biyu dake gabashin kasar.

An yi amfani da helicoptocin yaki da motocin sulke na soji a wannan farmaki da aka kai da hadin-gwiwar sojojin Congo a Rumangabo da Rugari dake arewacin Goma.

'yan tawayen suna kara dannawa ne a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi gwamnatin Rwanda da tallafawa 'yan tawayen, amma Shugaban Rwandar Paul Kagame ya musanta wannan zargi.

Mutane sama da dari biyu da hamsin fadan da aka fara cikin watan Aprilu ya sanya suka tsere daga gidajen su.

Karin bayani