Amurka ta nuna damuwa kan Aleppo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Aleppo a Syria

Amurka ta ce tana fargaba cewar sojojin Syria suna shirin aiwatar da kisan gilla a birnin Aleppo.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce akwai rahotannin da suka nuna cewar ana nufa birnin da tankunan yaki tare da kuma wani farmakin da ake kaiwa da manya da kananan jiragen yaki.

'yan tawayen Syria sun ce sune ke iko da a kalla rabin birnin na Aleppo, amma wakilin BBC dake bayan birnin ya ce a yanzu kowa na sauraren kazamin gumurzun da za a yi wanda babu daya daga cikinsu da zai yi sakacin shan kaye.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland ta gaya ma 'yan jarida cewar, alamomin a bayyane suke.

Karin bayani