Girka na cikin tsaka mai wuya kan kaidojin bashi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabannin tarayyar turai

Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Borroso ya shaidawa Prime Ministan Girka Antonis Samaras cewa lallai ne gwamnatin sa ta aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu muddin tana son a ba da bashin da zai ceto tattalin arzikinta.

Mr Borroso ya ce, maganar fatar baka ba ta isa ba.

Ranar Alhamis hannayen jarin kasashen Turai da Amurka sun yi matukar dagawa sakamakon kalaman da Shugaban Babban Bankin Tarayyar Turai Maria Draghi yayi.

Draghi ya ce bankin zai yi dukkan abinda zai iya, don kare darajar kudin euro.

Karin bayani