Ba a cimma matsaya ba kan sayar da makamai

Hakkin mallakar hoto x
Image caption Shugaba Obama

An tashi baram-baram a shawarwarin da ake yi na kulla yarjejeniyar kasa da kasa ta farko a kan batun sayar da makaman al'ada.

Kasar Amurka da Rasha da China sun ce suna bukatar karin lokaci da za su yi nazarin wasu batutuwa.

A karkashin yarjejeniyar da ake neman kullawa, ya zama wajibi ga kasashe su tantance ko makaman da za su sayar a iya amfani da su wajen keta hakkokin bil-adama ko kuma za su fada hannun kungiyoyin mutanen da ake aikata miyagun laifukka.

To amma duk da gazawar shawarwarin, Shugaban taron Roberto Garcia Moritan ya ce ya yi imanin za a sasanta zuwa karshen wannan shekarar.

Karin bayani