BBC navigation

Turkiyya ta ce dole a duba makaman Syria

An sabunta: 28 ga Yuli, 2012 - An wallafa a 07:18 GMT

Aleppo

Prime Ministan Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce dole ne a dauki mataki na kasa da kasa wajen tinkarar batun sojoji da makaman da Syria ke tarawa a kewayen birnin Aleppo.

Mr Erdogan yace duniya ba za ta cigaba da zama 'yar kallo ba.

Yana magana ne a wani taron manema labarai a London tare da Prime Ministan Britaniya David Cameron wanda yace Britaniyar da Turkiyya sun damu da irin yadda Syria ke shirin kaddamar da wasu ayyuka na ta'asa.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya nemi gwamnatin Syria ta fito ta yi bayanin cewa ba za ta yi amfani da makaman guba ba a kowanne hali aka shiga.

Jon lee Anderson na Mujallar New York wanda ya yi magana da BBC a bayan birnin Aleppo, ya ce mayakan 'yan tawayen suna shirin kare yankin dake hannun su.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.