Rikicin Kabilu a Habasha na da tarihi

Borana Ethiopia Hakkin mallakar hoto s
Image caption Yankin da ake takaddama

Kungiyar Red Cross a Kasar Kenya ta ce 'yan kasar Ehiopia fiye da dubu ashirin sun tsallaka kan iyaka don guje wa fadan da ake gwabzawa tsakanin wasu kabilu biyu dake gaba da juna.

Fadan wanda suke yi sakamakon jayayya a kan ikon mallakar filaye ya faro asali ne daga garin Moyale na kan iyaka a ranar laraba.

Kungiyar ta Red Cross tace sojojin Ethiopia sun shiga tsakani don dakatar da fadan, amma duk da haka mutane suka cigaba da tsallaka kan iyakar.

Yan kabilar Borana da Garri na gaba da juna tun shekara ta alif dari tara da casain da daya lokacin da ake kokarin kafa gwamnati bayan gwamnatin shugaba Mengistu Kaile Mariam ya rushe.

Karin bayani