Mutane tamanin sun rasu a Ambaliyar Korea

Koriya Hakkin mallakar hoto IFRC
Image caption Koriya ta Arewa ginin da ya rushe a ambaliyar ruwa

Rahotanni daga kafofin watsa labarai na Korea ta Arewa sun ce mutane tamanin da takwas sun hallaka cikin kwanaki goma sakamakon ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwar nan ta Khanun ta haddasa.

Rahotannin suka ce wasu mutanen fiye da dubu sittin sun rasa gidaje da gonaki da ambaliyar ruwan ta lalata.

Masu sharhi sun ce hasarar amfanin gonar za ta jefa mutane cikin matsananciyar wahala.

Korear ta arewa dama ta kan yi fama da karancin abinci.

Karin bayani