Romney: daidai ne Israila ta kare kanta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mitt Romney

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican a Amurka, Mitt Romney, ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyan Amurka ta hana Iran mallakar makaman nukiliya.

Yayin wani jawabi a birnin Kudus, ya ce Amurka ta gamsu da 'yan cin da Isra'ila take da shi na kare kanta, kuma ya kamata kasashen biyu su dauki dukkan matakai domin hana Iran kera makaman nukiliya.

Ya kuma ce, wauta ce ko kuma abinda ya fi haka idan aka dauki kalaman shugabannin Iran suka musanta an yi ma Yahudawa kisan kiyashi, ko suka tabo batun shafe Israila daga taswirar duniya, a matsayin maganganu ne kawai na fatar baki kawai.

Wakilin BBC ya ce yayin da ya rage kwanaki dari a gudanar da zaben shugaban Amurka Mr Romney na son nuna cewa zai iya daukar tsauraran matakai fiye da shugaba Obama kan harkokin kasashen waje.