Annan: A kafa sabuwar gwamnati a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Syria

Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Kofi Annan ya ce lamurran baya-bayan nan dake faruwa a birnin Aleppo sun nuna bukatar dake akwai ta kasashen duniya su tsoma baki don a kawo sauyin Shugabanci a kasar.

Wani wakilin BBC a birnin na Aleppo ya ce fadan da ake gwabzawa ya kaara muni a can, a yayinda sojojin gwamnati ke kara kaimi a hare-harensu na murkushe 'yan tawaye.

Farar hula na cigaba da kokarin tserewa daga birnin.

Tun farko, Ministan harkokin wajen Rasha Sergie Lavrov ya amince da cewar ana neman tafka abubuwan assha a birnin na Aleppo, to amma acewarsa, wani abu ne da aka san ba zai yiwu ba gwamnatin Syriar ta rungume hannu ta bar wasu masu rike da makamai a wurin.

Karin bayani