Mutane 20 sun rasu a gobara a India

Image caption Tasawirar Andhra Pradesh

Jami'ai a Kudancin India sun ce akalla mutane ashirin da biyar suka mutu sakamakon wata wuta da ta kama wani jirgin kasa.

An hangi wutar ne tana ci a daya daga cikin taraggon a lokacin da yake tafiya cikin garin Nellore dake jihar Andra Pradesh.

Wasu rahotanni sun ce wutar ta tashi ne bayan yankewar wayar lantarki.

Mutane da dama sun samu raunuka.

Karin bayani