Mata sun kai kara kan juyamusu mahaifa

Image caption Matan Namibia

Nan gaba ne a yau wani alkali a kasar Namibia zai yanke hukunci a kan ko an keta hakkokin wasu mata uku dake dauke da kwayoyin cutar HIV/ADS.

Matan dai na zargin an juya musu mahaifa ba tare da amincewar su ba.

An gaya wa matan cewar lallai ne su amince da haka idan har suna so ayi musu tiyata a fitar da 'ya'yan na su don rage hadarin yiwuwar kamuwar 'ya'yan na su da kwayoyin cutar ta HIV.

Wakilin BBC a Kudancin Afrika ya ce idan hukuncin ya baiwa matan gaskiya, zai yi matukar tasiri ga kasashe da dama na yankin wuraren da juya wa matan masu dauke da kwayoyin cutar HIV mahaifa ya zama jiki.

Karin bayani