Mutane hudu sun mutu a harin Sokoto

'Yan sanda a bakin aiki a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda a bakin aiki a Najeriya

A jihar Sokoto dake arewacin Najeriya mutane hudu sun mutu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a kan ofishin mataimakin Sifeton 'yan sanda mai lura da shiyya ta goma dake unguwar Marina.

Haka kuma an kai wani harin a kan Caji ofis dake unguwar Rogo.

Cikin wadanda suka mutu sun hada da 'yan kunar bakin wake biyu da dan sanda da kuma wata mace.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an garzaya da mutane sama da talatin zuwa asibiti sakamakon raunukan da suka samu.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da jama'a ke kai komo kuma da dama sun tsere domin neman mafaka sakamakon harbe-harben da suka biyo bayan harin.

Wadanda suka shaida al'amarin sun ce hayaki ya turnuke sama.