An kai harin kunar-bakin-wake a Sokoton Najeriya

MD Abubakar Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed D. Abubakar

Rahotanni daga Jihar Sokoto a arewacin Najeriya sun ce an kai wadansu tagwayen hare-haren kunar-bakin-wake a ofishin Mataimakin Sufeto Janar na 'Yansanda mai kula da Shiyya ta Goma da ke unguwar Marina, da wani caji ofis da ke unguwar Rogo.

Mutane sun yi ta tserewa domin neman mafaka sakamakon harbe-harben da suka biyo bayan hare-haren.

Wani wanda ya shaida faruwar al’amarin ya ce da misalin karfe 12 na rana ne wani “ya zo da mota kirar Honda—sabuwa—ya shiga hedkwatar ‘yan sandan Shiyya ta Goma ta kuma tashi bama-baman da ke ciki”.

Ya kuma kara da cewa hayaki ya turnuke har ba a iya ganin komai.

Wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross da ke Sokoto, babban birnin Jihar, ya shaidawa BBC cewa an garzaya asibiti da mutane shidan da suka yi raunuka sakamakon harin.

Kungiyar ta Red Cross ta ce mutane hudu ne suka mutu a hare-haren na Sokoto, yayin da mutane sama da talatin suka samu raunuka.

Matattun sun hada da 'yan kunar-bakin-waken biyu, da dan sanda daya da kuma wata mace.

Karin bayani