Babban jami'in Diplomasiyyar Syria a London ya yi murabis

Wasu mayakan 'yan tawaye a Aleppo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mayakan 'yan tawaye a Aleppo

Ma'aikatar hulda da kasashen waje ta Burtaniya ta ce babban jami'in diplomasiyyar Syria a London ya ajiye aikinsa.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce shugaban ma'aikatan ofishin jakadancin Syria a Burtaniya, Khaled al-Ayoubi ya ce ba ya son cigaba da wakiltar gwamnatin da ta ke zaluntar mutanenta.

Ajiye aikin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun gwamnatin Syria ke cigaba da ragargaza birnin Aleppo da ke hannun 'yan tawaye, ta hanyar amfani da jiragen yaki da manyan bindigogi.

Gwamnatin Syria ta ce ta kwace iko da gundumar Salaheddin, sannan ta kori dakarun 'yan tawayen, amma 'yan tawayen sun musanta hakan.

Karin bayani