Ku daina musabiha yayin gaisuwa —Yoweri Museveni

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda
Image caption Shugaba Yoweri Museveni na Uganda

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, ya gargadi al'ummar kasar da su daina musabiha yayin gaisawa sanadiyyar barkewar cutar Ebola wacce ta hallaka mutum guda a Kampala, babban birnin kasar.

Wacce ta rasun dai jami'ar jinya ce wacce aka kwantar da ita a asibitin Kampala bayan da ta kamu da Ebola a yammacin kasar ta Uganda, inda cutar ta hallaka mutane goma sha uku a makwanni ukun da suka gabata.

A wani jawabi na musamman da ya yi ta gidajen radiyo da talabijin, Mista Museveni ya yi kira ga jama’a su kula sosai:

“Ina rokonku da ku gaggauta kai rahoton duk wata cuta da ta yi kama da Ebola. Alamun dai sun hada da zazzafan zazzabi, da amai, wani lokacin da gudawa hade da zubar jini”, inji Shugaba Museveni.

Babu magani balle riga-kafin kamuwa da kwayar cutar ta Ebola, wacce ke hallaka kusan duk wanda ya kamu da ita.