Amurka ta nuna damuwa game da ayyukan sake gina Afghanistan

Sojojin Amurka a Afghanistan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Amurka a Afghanistan

Wani rahoton gwamnatin Amurka game da aikin gine-gine a Afghanistan ya gano cewa da yawa daga cikin ayyukan ba za su kammalu ba kafin lokacin da dakarun Amurka na karshe za su bar kasar a cikin shekarar dubu biyu da goma sha hudu.

Wakilin BBC ya ce a wani jawabi da babu kwane-kwane a cikinsa, babban sufeton da ke lura da ayyukan ya ce daga cikin dala miliyan dari hudun da aka fitar a bara, an yi asarar wani kaso mai tsoka saboda sakacin tsare-tsare, da kuma tafiyar da ayyukan.

An dai ware kudin ne domin samar da tituna, da gadoji, da kuma tashoshin samar da wutar lantarki, amma rahoton ya ce gwamnatin Afghanistan ba za ta iya cigaba da kula da mafi yawancinsu ba.

Karin bayani