Rana ta biyu ta katsewar wutar lantarki a India

Shagon wani aski yayinda aka dauke wuta Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shagon wani mai aski , bayan an dauke wuta

Wata matsalar karancin wutar lantarki ta jefa mutane kimanin miliyan dari shidda cikin duhu a kasar Indiya.

Rashin wutar na shafar jihohi goma sha uku, Kuma matsalar na shafar harkar sufurin jiragen kasa, da dibar kudi ta na'urar ATM, da kuma samun ruwan pampo.

An samu rahotannin katsewar wutan a jihohin Delhi da West Bengal da Jharkhand da Punjab da Rajasthan da kuma Bihar.

A yanzu haka kusan jiragen kasa dari sun tsaya cik, a yayinda Pasinjojin suka yi cirko cirko, ga shi kuma asibitoci da wasu ayyukan gaggawa son koma amfani da injunan janareto.

Hakan dai na zuwa ne kwana guda bayan da tashar samar da wutan lantarki ta arewacin kasar ta daina aiki na awoyi shida a jiya.

Bukatar da kasar Indiya keda ita na hasken wutan lantarki nada matukar yawa, ganin cewar tattalin arzikinta na kara bunkasa, abunda yasa masu sharhi ke ganin cewar idan har gwamnatin kasar bata kashe makudan kudade ba a bangaren na lantarki , tabbas za a cigaba da fuskantar katsewar wutan lantarki a sassan daban daban na kasar.

Karin bayani