An keta hakkin sojojin Mali

Shugaban riko na kasar Mali Hakkin mallakar hoto x
Image caption Shugaban riko na kasar Mali

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce sojoji masu biyayya ga hambararriyyar gwamnatin Mali sun fuskanci azabtarwa da keta hakki iri daban-daban a hannun sojojin da suka yiwa gwamnatin juyin mulki a watan Maris.

A cikin wani rahoto da ta fitar yau Talata, kungiyar ta ce wasu sojojin sun bace bat, wasu kuma an azabatar ko ma an halaka su a inda ake tsare da su.

A baya dai sojojin sun yi yunkuri ne na yin wani juyin mulkin na mayarda martani, a ranar talatin ga wata afrilu.

Karin bayani