Azumi ya sa an dakatar da wasu daga aiki a Paris

Musulmi a Faransa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Musulmi a Faransa

An dakatar da wasu Musulmi masu horar da wasanni a wani sansanin matasa da ke Faransa daga bakin aikinsu saboda yin azumi lokacin da su ke kula da yara.

Magajin garin Gennevilliers ya ce cin abinci a kan kari na daga cikin ka'idojin aikin.

Magajin garin ya kara da cewa shekaru uku da suka wuce wani yaro ya jikkata a hatsarin mota yayinda wata mai horarwa ta ba ta cin abinci ke tuka motar.

Wakilin BBC ya ce masu kare hakkin dan adam na cewa ma'aikata na da ikon cin abincin rana ko kuma a'a.

Haka kuma majalisar Musulmi ta Faransa ta sha alwashin marawa mutanen hudu baya a yayinda su ke neman hakkinsu a kotu.

Magajin garin Gennevilliers, dake wajen birnin Paris ya ce bai kamata a yi ma matakin da ya dauka kallon na nuna bambanci ba, domin zai dauki irin wannan mataki ko da mace ce ya samu tana kaurace ma abinci domin ta rage kiba.

A yanzu, wadannan musulmi hudu da aka dakatar, wadanda zasu ci gaba da karbar albashinsu, sun yi barazanar kai karar karamar hukumar a gaban kotu.