An fara bikin makon shayar da jarirai nonon uwa na duniya

Nonon uwa yana da muhimmanci ga jarirai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nonon uwa yana da muhimmanci ga jarirai

Wannan makon ne dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da kuma Asusun UNICEF, suka kebe domin kara fadakar da jamaa a kan muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zalla na tsawon watanni shida tun daga haihuwa.

Wani nazari da Asusun Kula d Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF y gudanar na nuni da cewa shayar da jarirai nonon uwa zalla na watannin shidan farko shi ne abin da ya fi kome muhimmanci wajen ci gaban jaririn ta fuskar lafiya da kuma dorewar rayuwarsa.

Hukumomin na duniya dai sun bayyana cewa kashi goma sha uku cikin dari ne na jarirai a Nijeriya ke samun shayarwar nonon uwa zalla har ya zuwa watanni shidda na farkon rayuwarsu.

Masana dai sun ce kara wayar da kan al'uma da ilmanatar da su da kuma kyautata koshin lafiyar iyaye mata na daga cikin matakan da ka iya taimakawa ga cimma burin shayar da jarirai nonon uwa a kasashe masu fuskantar koma baya a wannan fanni.

A shekara ta 1990 kasashen duniya suka amince a rika kebe daga ranar daya zuwa bakwai ga watan Agustan kowacce shekara domin bada muhimmanci ga shayar da jariran nunon uwa.

Karin bayani