An kama makamai a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan Najeriya

A Najeriya, rundunar da ke aikin wanzar da tsaro a jihar Borno- JTF, ta ce ta kama motar akori-kura dauke da makaman roka guda 8, da bama-bamai 10, da kuma kurtun alburusai guda 13, bayan da ta samu bayanan sirri.

Kakakin rundunar, Laftanal Kanal Sagir Musa, ya shaida wa manema labarai a Maiduguri cewa, a ranar Litinin ne rundunar ta kama makaman, sannan ta kashe mutane biyu cikin uku da ke cikin motar bayan da suka bude wa sojojin wuta, inda su kuma suka mayar da martani.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Dabar Masara da ke karamar hukumar Monguno kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Chadi.

Laftanal Sagir Musa, ya kara da cewa mutum na uku ya gudu, amma an samu bundugogi kirar AK47 guda biyu a wajen mutane biyun da aka kashe.

Karin bayani