'Mutane miliyan 18 ne ke fama da yunwa a Sahel'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani yaro da ke fama da cutar tamowa a Afurka

Wani rahoto da wasu kungiyoyin agaji guda biyu suka fitar ya nuna cewa fiye da mutane miliyan goma sha takwas ne a yankin Sahel da ke yammacin Afurka ke fama da matsalar rashin abinci ta din-din-din.

Rahoton, wanda kungiyoyin World Vision da Save the Children suka fitar, ya kara da cewa fiye da yara miliyan guda ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar yunwa.

Kungiyoyin sun ce ko da a shekarar da ba a fuskanci matsalar rashin abinci ba yara fiye da dubu dari biyu ne suka mutu a yankin saboda rashin samun abinci mai gina jiki.

Kungiyoyin sun ce rashin kariyar da talakawa ke fuskanta daga yawaitar tsadar abinci ne ke ta'azzara matsalar rashin abinci a yankin ba fari ba.

Shugaban kungiyar Save the Children, Justin Forsyth,ya ce akwai bukatar gano ainihin tushen matsalolin da ke kawo yunwa sannan a samo hanyoyin da za a magance su a taron da za a gudanar a birnin London game da yunwa a yankin Sahel bayan kammala gasar Olympics.

Karin bayani