Al Assad yayi tsokaci akan fadan Aleppo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Basar Al Assad

Yayin da gwawarmayar kwace iko da Aleppo birni mafi girma a Syria ke cigaba, shugaba Bashar Al Assad ya fadawa dakarunsa cewa, fadan kwace iko da Aleppo yana da matukar muhimmanci wajen fayyace makomar kasar da ma al'ummarta.

Sai dai kuma 'yan tawayen Syrian sun samu makamai masu linzami dake kakkabo jiragen saman yaki, kuma suna karfafa iko da wasu sassan birnin Aleppo, duk da cewa kafofin yada labarun gwamnati na cewa, dakarun gwamnatin sun yi mummunar barna ga wadanda suka kira, 'yan ta'adda dake dauke da makamai.

Kakakin tawagar majalisar dinkin duniya a Aleppo Susan Ghosheh ta tabbatar da cewa yanzu 'yan tawayen sun mallaki muggan makamai ciki har da tankunan yaki.

A yanzu haka dai yakin ya fi kazanta ne a Aleppo, inda masu fafutuka suka ce mayakan 'yan tawaye sun kwace ofisoshin 'yan sanda da dama.