Makomar Syria na cikin hadari - Assad

Shugaban kasar Syria, Bashar Al-Assad Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban kasar Syria, Bashar Al-Assad

Shugaban Syria Bashar Al-Assad ya yi gargadin cewa gumurzun da ake yi tsakanin dakarun 'yan tawaye da kuma na gwamnatin Syria ne zai tantance makomar kasar.

A wata sanarwa da aka fitar don tunawa da 'yan mazan jiya, Assad ya yabawa sojoji wajen yin fito-na- fito da wadanda ya kira gungun 'yan ta'adda masu dauke da makamai.

A baya-bayan nan dai an yi ta samun fafatawa a kan titunan birnin Damuscus da kuma birni na biyu mafi girma wato Aleppo.

Rahotanni na baya-bayan nan na nuna cewa a karon farko fada ya barke a kusa da unguwannin da Kiristoci ke zaune a tsohon birnin Damuscus.

Masu fafutuka dai sun kiyasata cewa kimanin mutane dubu ashirin ne suka rasa rayukansu tun fara tashin hankalin a watan Maris na shekarar da ta wuce.

Mako biyu kenan rabon da Assad ya yi jawabi a fili, gabannin fitar da sanarwar.