BBC navigation

Kofi Annan ya ajiye aikin wakilin kasa-da-kasa

An sabunta: 2 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:50 GMT
Kofi Annan

Wakilin Kasa-da-kasa a Syria, Kofi Annan

Wakilin kasa-da-kasa na musamman ga Syria, Kofi Annan, ya ajiye aikinsa na mai shiga-tsakani a madadin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Larabawa.

A wata sanarwa da ya fitar, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya ce Mista Annan ya yanke shawarar ba zai sabunta wa’adinsa ba: a karshen watan Agusta ne dai zai sauka daga mukamin.

Sanarwar ta zo ne a ranar da aka ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da ’yan tawaye a Damascus da Aleppo.

’Yan tawayen sun kaddamar da hari a kan wani sansanin sojin sama a kusa da Aleppo wanda dakarun gwamnati ke amfani da shi don kai hari da jiragen sama masu saukar ungulu a kan ’yan tawayen.

Masu fafutukar dake adawa da gwamnatin kasar ta Syria dai sun zargi dakarun gwamnati da mayakan sa kai wadanda ke goyon bayan gwamantin da aiwatar da kisan kiyashi a kan mutane fiye da saba’in.

Wakilin BBC a yankin ya ce wannan alama ce dake nuni da cewa fadan da ake tafkawa don kwace garin Aleppo zai dauki tsawon lokaci, bayan da wani bidiyo da masu fafutuka suka fitar ya nuna yadda ’yan tawaye a birnin na Allepo suka aiwatar da kisan kiyashi a kan mayakan sa kai dake goyon bayan gwamnati da aka kama.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.