An rantsar da majalisar ministocin Masar

sabon praministan Masar, Hesham Kandil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption sabon praministan Masar, Hesham Kandil

An ratsar da sabuwar Majalisar zartarwa ta Masar a fadar Shugaban kasa dake birnin Alqahira.

Sabon Praministan Masar, Hesham Kandil ya yi kira ga 'yan kasar da su nuna goyon baya ga sabuwar gwamnati domin shawo kan abun da ya kira manyan kalubale.

Majalisar ministocin mai wakilai talatin da biyar ta shugaba Mohammed Morsi za ta cigaba da aiki da wasu ministocin da suka yi aiki karkashin gwamnatin soja, ciki har da ministan tsaron kasar Fil Marshal Hussein Tantawi . Fil Mashal Tantawi Shi ne kuma ya jagoranci gwamnati wucin gadi har zuwa lokacinda aka zabi Mohammed Morsi a watan Yunin da ya gabata.

Sojoji dai na cigaba da rike ragamar iko a Masar ciki har da ikon yin dokoki.

Ministoci hudu ne kawai suka fito daga kungiyar 'yan uwa musulmi wanda shi ma shugaban kasar memba ne a cikin kungiyar.

Karin bayani