BBC navigation

Kira ga 'yan Nijar mazauna waje su zuba jari a gida

An sabunta: 2 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:36 GMT
Issoufou Mahamadou

Shugaba Issoufou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar

An fara wani babban taro a Jamhuriyar Nijar wanda ya hada 'yan kasar da ke zaune a kasashen waje.

Taron, wanda Ma'aikatar Harkokin Waje ta shirya zai baiwa 'yan kasar mazauna kasashen waje damar samun haske a kan manufofin gwamnati ta fuskar farfado da tattalin arziki da kyautata rayuwar jama'a.

Gwamnatin Nijar din dai ta shirya taron ne domin jawo hankalin ’yan kasar dake zaune a kasashen waje domin su zuba jari a gida da nufin bayar da tasu gudunmawar ga gina kasa.

A cewar Ministan Harkokin Wajen kasar, Bazoum Mohamed, “Abin da muka yi imani da shi shi ne ’yan Nijar mazauna [kasashen] waje mutane ne da idan aka ba su dama suna iya sa jari cikin kasa—ke nan ya kamata a san menene matsalolinsu, a kwatanta musu abin da ake ciki domin a nuna musu hanya; su ma su fadi irin matsalolin da suka fuskanta domin a magance musu”.

Ya kuma kara da cewa Ministan Kudi zai yi musu karin bayani a kan abubuwan da suka shafi kwastam (douane), da haraji.

“Za kuma a kwatanta musu menene tsarin nan na ‘’Yan Nijar Su Ci Da ’Yan Nijar, domin a cikinsu akwai masu sons u sa jari a [harkar noma]…”, inji Malam Bazoum.

Korafe-korafe

Wadansu daga cikin mahalarta taron sun bayyana cewa a shirye suke su zuba jari a kasar.

A cewar Idris Abdoullahi, wanda ya halarci taron daga birnin Paris na kasar Faransa “[A shirye muke] kwarai da gaske—ni tuni ma na fara, domin ina kawo motoci, kuma ina gini ina sa haya, kuma ina da [kungiya mai zaman kanta] wadda [ta hanyarta] ina aiko magunguna, da kayan [bincike a] makarantu, da kudi don a yi rijiyoyi a taimakawa talakawa”.

Sai dai kuma shugaban ’yan Nijar mazauna Najeriya, Alhaji Abubakar Khalidu, ya koka cewa da dama daga cikin ’yan Nijar sun gwammace sun mutu da dukiyoyinsu a waje.

“In ka tallafo dukiyarka za ka zo gida, daga bakin iyaka sai gwammace ka ajiye ka sake komawa—a nan ma na bude kamfani, na kuma samu akalla shekara Daya da wani abu sai na sake rufe shi saboda harajin da ake dora mana ba za mu iya ba”, inji shi.

Firayim Minista Brigi Rafini ne ya jagoranci bude taron a madadin Shugaba Issoufou Mahamadou.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.