An yi tur da kisan da aka yi wa magoya bayan gwamnati a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan tawaye a Syria

Kungiyar 'yan adawar Syria ta soki 'yan tawayen da suka hallaka fursunonin da suka kama masu goyon bayan gwamnati a birnin Aleppo.

Kungiyar ta ce duk da yake magoya bayan gwamnatin sun aikata laifuka inda suka rika kashe 'yan tawaye, amma ta ce bai kamata a kashe su ba.

A cewar kungiyar mai suna, Syria National Council a turance, kisan da aka yi wa magoya bayan gwamnatin ramuwar gayya ce a kan azabtarwar da suka yi wa 'yan Syria.

Wani gungun 'yan bindiga ne dai ya kama wani shugaban 'yan kungiyar da ke goyon bayan gwamatin, da wasu magoya bayansa, kana suka tasa keyarsu zuwa jikin wani bango, inda suka jera su, kana suka bude musu wuta.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta ce abin da aka yi na kama da laifukan yaki.

Sai dai Abdullah Omar, dan uwan wani mutum da magoya bayan gwamnati suka kashe, ya ce bai kamata a dorawa wata kungiya alhakin kisan ba.

Ya ce: ''ba karya ba ne cewa ana aikata irin wannan laifi, to amma ya kamata ka tsaya tsaka tsaki. Bai kamata ka kimanta dukkanin bangarorin a matsayi daya ba.

Fada ya kazanta a Aleppo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikici a birnin Aleppo ya kazanta cikin sa'oi saba'in da biyun da suka gabata.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a Syria, Susan Ghosheh, ta tabbatarwa BBC cewa mayakan 'yan adawa sun samu manyan makamai, ciki har da tankunan yaki da suka kwace.

Ta ce:''rikicin da ke faruwa a Aleppo ya yi matukar tayar mana da hankali. A halin yanzu ana dauki-ba-dadi tsakanin bangarorin biyu.Masu sa-idon da muka aika sun ce ana musayar wuta. Sun kuma ce ana amfani da jirage masu saukar ungulu da tankokin yaki da manyan bindigogi da kuma bama bamai''.

Karin bayani