Syria: Dalilan da suka sa Annan ajiye mukaminsa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kofi Annan

Wakilin kasashen duniya a Syria, Kofi Annan, ya ce taurin kan shugaba Bashar al Assad ne babban dalilin da ya sanya ya ajiye aikinsa na mai sasanta wa a rikicin kasar.

Mista Annan ya ce a duk lokacin da ya gabatar da hanyoyin da yake gani za a bi don magance rikicin Syria shugaba Assad na yin watsi da su ba tare da yin la'akari da muhimmancinsu ba.

A cewarsa, 'yan adawar kasar sun taka muhimmiyar rawa wajen ba shi wuya a lokacin da yake gudanar da aikinsa, domin kuwa ba su ajiye makamansu ba yayin da suka yi alkawarin yin hakan.

Kazalika, Mista Annan ya ce duk da goyon bayan da shirinsa na magance rikicin Syria ya samu daga daukacin kasashe mambobin kwamatin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kasashen sun gaza warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu a kan yadda za a tunkari matsalar kasar.

Kasashen yammacin duniya ba su gushe ba dangane da bukatarsu ta ganin an samu sauyin gwamnatin a Syria, a yayin da suke matsa lamba don sanyawa kasar takunkumi.

A gefe guda kuma, Russia da China sun dage cewa bai kamata kasashen duniya su yi katsalandan a harkokin cikin gida na kasar Syria ba.

Majalisar Dinkin Duniya za ta kada kuri'a

A ranar Juma'a ne Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuria game da wani kuduri da ke Allah-wadai da gazawar Kwamitin Sulhu na Majalisar wajen daukar mataki kan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Kasar Saudiyya ta goyi bayan daftarin kudurin, wanda ya nuna goyon baya ga 'yan tawayen Syria.

Za a kada kuri'ar ce, kwana guda bayan da Kofi Annan ya bayar da sanarwar ajiye aikin shiga tsakani a Syria.

Kofi Annan ya ce ya kamata kasashen duniya su sauya salo wajen tunkarar rikicin, don tursasawa bangarorin guda biyu su zauna kan teburin shawarwari.

Karin bayani