Hillary Clinton ta ziyarci Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta yi kira ga Sudan da Sudan ta Kudu da su warware bambance bambancen dake tsakaninsu kan rabon arzikin man petur, matakin dake neman durkusar da kasashen biyu.

Lokacin da take jawabi a ziyararta ta farko a Sudan ta Kudu, Mrs Clinton ta ce akwai bukata cikin gaggawa bangarorin biyu su cinma yarjejeniya a tattaunawar da ake yi a Ethiopia , tun tattalin arzikin kasashen biyu na like da juna.

Sakatariyar harkokin wajen Amurkar ta koma Uganda domin ganawa da Shugaba Yoweri Museveni.

Tattaunawar zata mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi tsaro a Somalia da Congo, da kuma kokarin kama jagoran 'yan tawayen nan, Joseph Kony.

Mrs Clinton ta fara ziyarce da kasar Senegal, inda ta yi kira ga shugabannin kasashe masu yi ma karagar mulki rikon, mutu-ka-raba da su rungumi tsarin dimokradiyya, su kuma sakar ma al'umominsu mara, ta fuskar tattalin arzikin kasa.

Ta kara da cewa mulkin kama-karya, da kaifin kishin addini, da kuma cin hanci da rashawa na daga cikin abubuwan dake yi ma mulkin dimokradiyya tarnaki a nahiyar Afrika.

Ziyarar ta kasashe bakwai, zata kwashe kwanaki goma sha daya tana yi.

Karin bayani