Tseren kwale-kwale: Dan Nijar Issaka ya samu tagomashi

Dan tseren kwale-kwale daga Nijar Hamadou Issaka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan tseren kwale-kwale daga Nijar Hamadou Issaka

Dan tseren kwale-kwale daga Nijar Hamadou Djibo Issaka ya samu tagomashi da kyakyawar tarba daga taron 'yan kallo a Eton Dorny, duk kuwa da cewa shi ne ya zamanto kurar baya a gasar tseren kwale-kwale ta maza.

Dan wasan mai shekaru 35, wanda a yanzu ake yi wa lakabi da "Issaka the Otter", ya kammala tseren ne a cikin kimanin mintuna tara.

Issaka ya fara tseren kwale-kwale ne watanni uku kacal da suka gabata, ya kuma samu horon fitowa a olympics ta hanyar amfani da wani tsohon kwale-kwale na kamun kifi.

A yanzu yana shirin shiga a dama da shi a gasar Olympics mai zuwa ta shekarar 2016 da za a gudanar a Brazil.

Duk da cewa Issaka ya zo na karshe a gasar, amma za a iya cewa ya tabuka wani abu, kasancewar ya fito ne daga kasar da ba ta yi iyaka da teku ba kuma take cike da sahara.

Kafin gasar ta Olympic, Issaka yana aikin kula da lambu da kuma wani wurin iyo a Yamai babban birnin kasar sa Nijar.

A hira da manema labarai,dan wasan ya shaida musu cewa "Ba ni da kwarewa" amma ina amfani da karfi, mutane da dama sun nuna min goyon baya, sun tafa min."

Ya kuma ce a yanzu mutane da dama a Nijar na can na jiransa da ya koma ya koya musu tseren na kwale-kwale.

Karin bayani