BBC navigation

An gano sababbin rijiyoyin mai a Nijar

An sabunta: 3 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 06:51 GMT

Issoufou Mahamadou

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Alhaji Issoufou Mahamadou, ya ce an gano wasu sababbin rijiyoyin mai a yankin Agadem na kasar kuma akwai alamomin da ke nuna cewa a yankin Bilma ma za a samu wani dimbin man.

Shugaba Issoufou Mahamadou ya bayar da wannan sanarwa ce a cikin wani jawabi da ya yi wa 'yan kasar a ranar Alhamis da daddare domin bikin cikar kasar shekaru 52 da 'yancin kanta.

Shugaban ya ce: '' Zan yi amfani da wannan dama na sanar da 'yan kasa cewa an gano wani dimbin mai a yankin na Agadem, sannan akwai kyakkyawar alama ta samun mai a yankin Bilma.Gwamnati na ci gaba da tattauna wa da kasashen Chadi da Cameroon dangane da aikin jawo bututun man da zai ratsa ta kasashen domin sayar da shi a kasashen waje.''

Shugaba Issoufou ya kara da cewa hakan ya sanya kasar cikin jerin kasashen duniya da ke alfahari da samun albarkatun mai.

A cewarsa, za a yi amfani da kudin da za a samu idan aka sayar da fetur din wajen inganta rayuwar al'umar Nijar.

Shugaba Issoufou ya ce gwamnati ta fara ginin hanya wacce ta taso daga jihar Diffa zuwa Gigimi har ma zuwa kan iyakar Nijar da kasar Chadi.

Ya ce nan gaba za a gina hanya daga Bilma ta biyo ta Agadem da Ungurti, kana ta isa Gigimi, kuma za a sanya wa hanyar suna ' hanyar man fetur'.

Shugaba Issoufou ya yi kira ga 'yan Nijar da su kara ba shi hadin kai wajen gina kasa da bunkasa tattalin arzikinta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.