Kotun kolin Pakistan ta yi watsi da dokar kare jami'an gwamnati

Pakistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kotun kolin Pakistan

Kotun kolin Pakistan ta yi watsi da wata doka wadda ba a dade da amincewa da ita ba, wadda ta ke bada kariya ga manyan jami'an gwamnati daga aikata laifin raina kotu.

Alkalan kotun biyar, karkashin jagorancin babban mai shari'a , Iftikhar Muhammad Chaudhry , sun ce bada kariya ga masu rike da mukaman gwamnati ya saba kundin tsarin mulki.

Majalisar dokokin Pakistan ta amince da dokar ce a watan Yuli, bayan da kotun ta kori ,Yousef Raza Gilani, bisa zargin aikata laifin raina kotu.

Masu sharhi kan al'amurran yau da kullum sun ce wannan mataki da kotun ta dauka zai iya yin sanadiyar sauke praministan kasar ta Pakistan mai ci yanzu, Raja Pervez Ashraf.

Karin bayani